Najeriya Zata Dauki Mataki Kan Kisan Yan Kasar Ta A Afrika Ta Kudu

nig flag2 small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa Najeriya zata dauki mataki kan kisan yan Najeriya dake zaune a kasar Afrika ta Kudu.

Onyeama, ya bayyana hakan a shafin sa na Twitter inda ya bayyana jami’an yansandan kasar a matsayin mara sa amfani.
Ana cigaba da wallafa labaran a shafin ta yadda ake kona shagunan yan Najeriyan da kwashe kayan dake shagunanan yan najeriyan ba tare da daukar mataki daga yansandan kasar ba.

jami’an yansandan kasar sun dade suna kaiwa yan Najeriya hare-hare a kasar ta Afrika ta kudu dasu da bata garin kasar musamman a kwanakin nan.

Related stories

Leave a Reply