Najeriya: Zakzaky Da Matarsa Sun Dawo Daga Kasar Indiya

zakzaky
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Gwamnatin tarayya tace shugaban yan Shi’a na kasar nan Ibrahim El-Zakzaky tare da mai dakinsa sun dawo kasar nan daga kasar India bayan rashin da’a da suka nuna a tarin diplomasiyya tsakanin kasar nan da kasar India.

gwamnatin ta kara da cewa yayin da yake kasar India El-Zakzaky ya tuntubi manyan lauyoyin kasar kuma da sauran kungiyoyi masu zaman kansu wadanda suka hada da Islamic Human Rights Commission da sauran kungiyoyin Shi’a wadanda zaiyi amfani dasu ya nemi mafaka don sulalewa zuwa kasa.

A wata sanarwa da babbar sakatariya a ma’aikatar yada labarai ta tarayya Grace Isu Gekpe, tace dukkanin wadan nan halaye da Sheik Zakzaky ya nuna a kasar indiya sun yi nuni da irin kudurinsa na muzanta Najeriya da mai masaukinsa wato kasar India

Related stories

Leave a Reply