Najeriya: Za’a Biya Albashin N-Power Wani Satin – Imoukhuede

Mr Afolabi Imoukhuede, mataimaki na musamman kan samar da ayyuka da bada tallafi ga shugaban kasar najeriya ya bayyana cewa masu amfana da N-Power zasu karbi albashinsu na watan Maris wan nan satin.

Imoukhuede ya bada tabbacin ne ranar Alhamis a Abuja yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na NAN.
N-Power shiri ne na gwamnati don taimakawa mara sa aikinyi, ya kara da cewa suna nan suna wasu shirye-shiryen bada tallafi da koya sana’oi wanda zai tafi da tattalin arziki.

N-Power ta kunshi daukar matasa 500,000 da suka gama karatu aiki do cike wasu gurabu a bangaren ilimi, lafiya da sauransu.

Ya kara da cewa rahoto ya same su cewa wasu na ganin rashin biyan kudin na watan Maris kamar wata makarkashiya gwamnati take so tayi musu don ta cire su daga aikin.

NAN ta rawaito cewa ma’aikatan na samun albashinsu kowa ne karshen wata amma har yanzu na watan Maris shiru kuma basuji wani bayani daga mahukuntan ba.

Imoukhuede ya danganta wan nan tsaiko da matsalar da aka samu daga ma’aikatar kudi da kuma ofishin akanta na kasa amma yanzu komai ya dai-daita ba kamar yadda ake yadawa cewa ana so a cire wasu ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *