Najeriya: Yansandan Jihar Borno Sun Kama Sojoji 5 da Wasu 83 da Zargin Fashi Da Makami

Rundunar yansandan jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya ta kama sojoji 5 da wasu mutane 83 da zargin yin fashi da makami da kuma wasu laifuka.

Kwamishinan yansanda na jihar Mohammed Aliyu ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar dasu ga manema labarai ranar Alhamis a Maiduguri.

Ya kara da cewa an kama sojojin a gurare daban-daban, Aliyu yace an kama Hilary Oziama ranar 13 ga watan Mayu bayan ya hada baki da wani mai suna Kolawale Samuel inda sukayi wa wani mai suna Ibrahim Mohammed fashin keke mai kafa uku wanda yakai kimanin Naira 600, 000.

Sai wani mai suna Tgwe Sylvester wanda ya hada baki da Nnamani Micheal Bayo inda suka kwace mota a karamar hukumar Bayo.

Haka nan Rapheal Akintola jami’in Nigerian Security and Civil Defence Corps an kama shi da harsashai 60 a tashar mota ta Maiduguri.

Haka nan an samu wasu harsashan 237 a karkashin gadar kwastan dake birnin Maiduguri.
Kwamishinan ya kara da cewa sun kuma kama masu garkuwa da mutane a Askira Uba bayan sun karbi Naira miliyan 1.6 daga wanda suka kama Sale Hamman, wadanda ake zargi sune Ibrahim Usman, Ahmadu Hamman, Sule Hamman and Hamman Abdulrahaman.

Sai wani dilan kwayoyi Charles Noah da jami’an yansanda suka kama a Maiduguri da kayan maye da ya kai na kimanin Naira miliyan 2 inda aka wace kwayoyi da dama hade da kama wasu.

Haka nan rundunar ta kama wasu masoya biyu Shettima Bukar da Saude Saleh da suka kashe jaririn da suka Haifa a Maiduguri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *