
‘Yansandan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja sun dakile wani mummunan kutse da ‘yan shi’a sukayi zuwa majalisar kasar ranar Talata kan a sakar musu shugabansu Ibrahim El-Zakzakky.
A baya dai kungiyar sun fara gudanar da zanga-zanga ta lumana inda daga baya ya juce ya koma na tashin hankali inda suka yi yunkurin cusa kai majalisar kasar.
Yansandan dake aiki sunyi kokarin hana su inda suka tarwatsa su ta hanyar da ya dace, haka nan yan kungiyar sun harbi yansanda guda 2 a kafa, inda suka jefi wasu yansanda 6 da dutsina wanda har yayi sanadiyyar suka samu raunuka.
Tuni dai aka garzaya da yansandan da suka samu raunuka asibiti, kuma aka kama yan kungiyar su 40.
