Najeriya: Yansanda Sun Cafke Wadanda Suka Yi Garkuwa Da Ma’aikacin Channels

Yansandan Najeriya sun samu nasarar cafke mutanen da sukayi garkuwa da ma’aikacin gidan talabijin na channels inda suka samu makamai da dama.

Yansandan da suke aiki da Operation Puff Adder don bada bayanan sirri ne suka kama mutanen 3 da ake zargi dayin garkuwa da ma’aikacin Mr. Friday Okeregbe.

Wadanda ake zargin sune Hanniel Patrick shekara 29 daga jihar Akwa Ibom sai Abdulwahab Isah shekara 28 years da Salisu Mohammed mai shekara 32 duk daga jihar Kogi.

Haka nan bincike ya nuna ba Mr. Okeregbe suka so kamawa ba, amma, ida suka kaishi wata maboyarsu a Karmo a Abuja, inda suka samu makami,adda, wayoyi da kuma abin da suke rufewa wadanda suka kama fuska.

Haka nan jami’an sun kama wasu a hanyar Abuja zuwa inda suka samu makamai da dama. Shugaban yansandan kasa M. A. Adamu ya jaddada bada taimakonsa ga jamia’an nasa inda ya tabbatar cewa kwa nan nan za’a kawo karshensu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *