Najeriya: Yansanda Sun Kama Luba Udoka Jonah Mai Aika Sakon Banki A Jihar Neja

police-logo1
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Rikakken dan danfarar nan Luba Udoka Jonah wanda yak ware wajen damfarar mutane ta hanyar aika musu sakamakon banki na bogi ya shiga hannun jami’an yansanda dake jihar Neja.

An kama Onah bayan yayi yunkurin damfarar wani mai sai da motoci a Minna. Wanda ake zargin ya tabbatar da cewa yana aika sakon banki na bogi yayin da aka gudanar da cinikayya dashi.

Ya kara da cewa yana amfani da sakon bankin na bogi ya sai kaya masu matukar tsada sai ya bar gurin da sauri kafin a gane damfara yayi.

Mai magan da yawun rundunar ta hanyar yada labarai Muhammad Abubakar ya kirayi jama’a dasu kiyaye da irin wan nan cinikayya.

Related stories

Leave a Reply