Najeriya: Yanbindiga Sun Kashe Yan Kungiyar Sa Kai 6 A Jihar Zamfara

By: Hadiza Garba

Yan bindiga sun kashe yan kungiyar sa kai 6 a jihar Zamfara a karamar hukumar Shinkafi dake jihar Zamfara Sunday, inji mataimakin karamar hukumar Sani Galadima.

Sani Galadima ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi ministan cikin gida made this Abdurrahman Dambazau, wanda ya kai musu ziyara jihar a kokarin da gwamnati takeyi na ganin an kawo karshen rashin tsaron.

An kashe yan kungiyar ta sa kai bayan sun dawo daga karbar albashinsu a shikafi kan hanyar komawa kauyukansu.

Sani Galadima ya bayyana cewa kimanin kauyuka 98 ne dake Shinkafi suka gudu suka bar gidajensu.

Yayin da yake jawabi a karamar hukumar Anka Abdulrahman Dambazau ya bayyana cewa ya ziyarce su ne ya ganewa idonsa yadda abun yake kuma ya bayyana musu irin damuwar da shugaba Muhammadu Buhari yayi kan lamarin.

Sarkin Shinkafi Muhammad Makwashe-Isah ya bayyana jin dadinsa da godewa ministan kan ziyarar da ya kai musu haka nan ya kirayi gwamnatin kasar ta zage dantse.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *