
Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila tare da wasu daga cikin yan majalisar sun kawo ziyarar gani da ido jihar Borno domin hada kai da gwamnatin jiha domin a samu hanyoyin warware matsalar tsaro.
Bakin za su ziyarci sansanin yan gudun hijira dan su duba irin halin da suke ciki domin a kawo musu dauki.
Gwamna Zulum, a yayin da yake karbar su a gidan gwamnati, yace aiyukan BH ya jawo koma baya a fannin cigaban jihar Borno. Ya kara dacewa baza a taba samun cigaba ba idan babu zaman lafiya.
Yayi amfani da wannan dama dan yin kira ga shugaban majalisar da a kara karfafa aiyukan jami’an tsaro da kuma na civilian JTF.
Gwamnan yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake gina hanyoyin da suka tashi daga Maiduguri zuwa Gamburu Ngala, Maiduguri, Banki, Gwoza zuwa Askira, sai kuma Maiduguri zuwa Biu, da kuma Maiduguri zuwa Kukawa.
