Najeriya: Yan Gudun Hijira Sun Gudanar Da Zanga-Zanga Kan Karancin Abinci A Banki Dake Karamar Hukumar Bama A Jihar Borno.

borno
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Dubban yan gudun hijira ne suka gudanar da zanga-zanga sakamakon rashin abinci a sansanin dake Banki a karamar hukumar Bama a jihar Borno.  

Masu zanga-zangar sun fusata inda suka jefi wasu daga cikin ma’aikatan bada agajin hade da lalata ofishin majalisar dinkin duniya dake yankin.

Banki gari ne dake da iyaka da kasar kamaru kuma yana da nisan kilomita 138 daga gabashin Maiduguri babban birnin jihar.

Manaja mai kula da sha’anin tsaro na CARE International LassinaTraore ne ya bayyana hakan a Maiduguri, inda yace yayin rabon abincin ba’a basu mai ba wanda hakan ne ya haddasa zanga-zangar.

Traore ya bayyana cewa sabida gujewar faruwar hakan a nan gaba an kawo ma’aikatan tsaro sansanin wanda hakan yasa aka bar zanga zangar kuma aka kama wasu yan gudun hijirar.

Ya kara cewa suna kai kayan abincin gurin ajiya saboda har azo a kwashe a sansanin.

Related stories

Leave a Reply