
Sashen dake kula da harkokin bada agaji na majalisar dinkin duniya a kasar nan, yaji takaicin kai harin da aka yiwa yan tawagar bada agajin gaggawa inda yayi sanadiyyar mutuwar mutum 1 kuma wasu 6 suka bace a jihar Borno.
Ankai wannan harin ne yayin da tawagar bada agajin suka tashi daga Maiduguri zuwa garin Damasak.
Sakamakon hakane ofishin kula da yan agajin ke kira ga jama’a da su daina yada jita-jita saboda hakan yana sa rayuwar masu bada agaji cikin hadari.
