Najeriya: Yan Bindiga Sun Kai Hari Kauyen Nding A Jihar Plateau

boko-haram-336566-big
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

An kashe mutane 2 inda mutane 5 suka samu raunuka a sabon harin da yan bindiga suka kai kauye Nding dake karamar hukmar Barikin Ladi a jihar Plateau.

Abin ya faru da karfe 7 na dare, kuma hakan ya zo bayan hakan ya faru da makotansu dake Foron inda aka kashe mutuum 3 da shanu fiye da 200 suma sukayi awon gaba da dabbobi.

Senatan dake wakiltar arewacin Plateau a majalisar kasa Istifanus Gyang ya fitar da rahoto wanda mataimakinsa na musamman kan yada labarai, Musa Ashoms ya sawa hannu inda ya bayyana rashin jin dadinsa kuma yayi Allah wadai da harin.

Senator Gyang wanda shine mataimakin shugaban kwamitin kan sha’anin tsaro ya bayyana hare-haren a matsayin abu mara dadi.

Haka nan yansandan jihar basu tabbatar da faruwar lamarin ba.

Related stories

Leave a Reply