Najeriya: Wata Mata Ta Kashe Mijinta A jihar Kebbi

kebbi
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wata mata a karamar hukumar Bagudo dake jihar Kebbi ta kashe sabon mijin data aura don ta samu ta koma gidan tsohon mijinta.

A rahoton da yansanda suka fitar sun bayyana cewa wadda ake zargin, Auta Dogo Singe ta hada baki da wasu masu suna Garba Hassan da Sahabi Garba dake kauyen Sabon Gari a yankin Illo dasu kashe mijin nata mai suna Abdullahi Shaho don ta samu ta koma gidan tsohon mijinta.

Yayin da yake ganawa da manema labarai a hukumar yansandan dake Birnin Kebbi, kwamishinan yansandan Garba Muhammed Danjuma ya bayyana cewa tsohon mijin matar shine, Idris Garba wanda ke zaune a kauyen Tugar Bature dake yakin Illo.
Tuni dai aka kama matar da kuma mutane biyun data hada baki dasu.

A wani labarin kuma kwamishinan ya kara da cewa wasu masu suna Yahuza Ibrahim dake kauyen Gotomo a Argungu, Murtala Abdullahi, Malam Nasiru da Dansilami, sun shiga gidan wani mai suna, Adamu Yaro mazaunin unguwar Kalgo da muggan matakai inda suka yi masa fashin babur dinsa wanda yakai kimanin naira 253,000 da kuma wasu kayyayakin. Inda yace dukkansu na hannun hukuma.

Related stories

Leave a Reply