Najeriya: Wasu Dalibai Sun Nuna Rashin Da’a Yayin Jarrabawar A Jihar Borno – JAMB

BY: Habiba Ahmed

Ofishin zana jarabawar JAMB dake birnin Maiduguri a jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya ya bayyana rashin jin dadi da rashin da’ar da wasu daliban suka nuna yayin zana jarrabawar a wan nan shekarar.

Farfesa Babagana Gutti na jami’ar Maiduguri, bangaren fasaha wanda yake wakiltar JAMB ya bayyana wa Dandal Kura cewa an gudanar da horarwa ga daliban kan yadda za’a gudanar da jarrabawar amma wasu basu halarta ba, wasu hankalinsu na kan wayar su wasu kuma suna zuwa ba da wuri ba.

Ya kara da cewa JAMB ba zata gajiya ba wajen gyara kurakurenta don ganin an samu sauki a wata jarrabawar da za’a gudanar, haka nan ya kirayi iyaye da sus a ido kan yayansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *