Wasu Bata Gari Na Son Su Kawo Cikas Din Tsaro A Najeriya

Rundunar sojin Najeriya sun bayyana cewa sun lura cewa akwai wasu bata gari, kungiya da kuma yankasashen waje da suke so su kawo cikas din tsaro a yankin yammacin Afrika.

Mai Magana da yawun rundunar Kanal Sagir Musa ne ya bayyana hakan ba tare da ya bayyana mutanen da kungiyar ba inda yace suna so suyi amfani da yan ISWAP, Boko Haram da kuma yan ta’adda su basu kudade da taimakon ganin sun kawo cikas din.

Ya kara da cewa majiya mai karfi ta bayyana musu cewa wasu mutane sun hada kai Boko Haram, wasu kuma suna yiwa jami’an sojin sharri don su hada su da jama’a da kuma gwamnati.

Musa ya bayyana cewa suna nan sun kirayi masu wadan nan halayen dasu kiyaye wadan nan halayen ko su fuskanci daga hukuma.

Haka nan ya kirayi duk wasu da suke da wata kulalliya dasu yi kokari su sasanta banbancin dake tsakaninsu domin najeriya kas ace mai dokoki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *