Najeriya: Wani Pastor Da Wani Dan Bautar Kasa Sun Roki Gwamnati Da A Ceto Su Daga Hannun Yan Kungiyar Boko Haram

bh larrge
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wani Pastor mai suna Moses Oyeleke Emmanuel na cocin Living Faith Church da kuma wani dan bautar kasa mai suna Abraham Amuta sun nemi taimako da a ceto su daga kangin yan kungiyar Boko Haram.

Pastor dad an bautar kasar sun bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo wanda and Nigeria news magazine ta gani.

An kama mutanen biyi ne ranar 10 ga watan Aprilu na shekarar 2019 kusa da kauyen Yale dake karamar hukumar Konduga akan hanyarsu ta Chibok don raba kayan agaji wanda cocinsu ta Living Faith Church ta samar.

Emmanuel and Amuta sunyi rkiran ne tare da wasu dalibai mata 2 wadanda aka kama a garin Askira Uba.

Duk da dai ba’a tabbatar da cewa daliban yan makarantar AskiraUba bane amma paston dad an bautar kasar an tabbatar dasu.  

Wadanda aka yi garkuwa dasun sun yi kira ga shugaban kasa Muhammad Buhari day a taimaka musu ya ceto rayuwarsu. Har yau cocin da hukumar yiwa kasa hidima basu ce komai ba akan lamarin.

Yan kungiyar ta Boko Haram sun fito da wata hanya tayn garkuwa da mutane inda suka fara kama mutanen da basujiba basu gani ba  duk da an bayyana cewa wasu daga cikin yan matan Chibok dake hannunsu bama sa son dawowa amma mutane kamar Pastor Emmanuel da Amuta da Leah Sharibu na rokar gwamnati da masu ruwa da tsaki dasu ceto rayuwarsu.

Related stories

Leave a Reply