
By: Hadiza Garba
Hukumar Victim Support Fund ta kashe Naira miliya 130 wajen farfado da kuma sababbin ayyuka a gidan kangararru a birnin Maiduguri dake jihar Borno a arewa maso gabshin Najeria.
Daraktan hukumar Prof. Sunday Ochoche ne ya bayyana hakan yayin bikin gudanar da ayyukan a unguwar Bulum Kutu dake jihar.
Ochoche yace ayyukan an shirya su ne don karfafa ayyukan gurin don a samu a gyara halayen wadanda ake tsare dasu din da kuma koya musu ayyukan da dasu kula da kansu musamman wadanda rikicin ta’addanci ya shafa.
Yya kara da cewa ayyuakan da suke ciki sun hada da dakunan mata 5, na maza 5 dagayen azuzuwa guda 2, manyan dakunan mazauna gurin, hanyoyi da ofisoshin ma’aikata.
Sai Katanga mai tsaro, gyaran rijiyar burtsatsai, kayan motsa jiki da hada injin bada wutar lantarki.
Profeesor Sunday ya kara dacewa suna gudanar da ayyukan da gwamnatin jihar ta bangaren ilimi, gine-gine, da kuma wasu ayyukan da suka shafi jama’a saboda rikicin ta’adddanci.
Alhaji Tijjani Tumsa mataimakin shugaban kwamitin shugaban kasa wato PCNI, ya yabawa hukumar ta VSF saboda wan nan kokarin
Haka nan kwamishinar mata a jihar Hajia Fanta Baba-Shehu ta bayyana ayyukan a matsayin abinda yazo akan lokacin da ya kamata.
