Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Najeriya Ta Samu Mafi Karancin Masu Dauke Da Cutar COVID-19

Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

A ranar Lahadi ne Najeriya ta samu mafi karancin masu kamuwa da cutar Coronavirus a shekarar nan.

Inda kasar ba ta samu rahoton wadan da suka rasu ba sakamakon cutar data yadu a kasar tun 27 ga watan Fabarairu na shekarar 2020.

Rahotannin na Cikakkun bayanan suna cikin bayanan da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya ta bayar ta shafinta na Twitter ranar Lahadi.

A cewar hukumar da ke jagorantar yaki da cutar sabbin can samu mutane 86 da suka kamu da cutar a babban birnin tarayya da kuma wasu jihohi shida.

Babban birnin tarayya nada mutane 33, yayin da jihar Legas take da 28 sai kuma jihar Ondo 11. Sauran wadanda suka kamu da cutar sun hada da Kano-7, Akwa Ibom-3, Rivers-3 da Kaduna-1 Ya zuwa daren Lahadin, kasar ta rubuta adadin mutane 161,737 da aka tabbatar da cutar ta COVID-19 ta kama su, inda aka sallami 147,899 yayin da mutane 2,030 suka rasa rayukansu.

Leave a Reply