
Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin sarkin kasar Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al-thani wanda ya nemi zuba jari a bangaren mai, wuta, zirga-zirgar jiragen sama da kasa da kuma wasu guraren.
Haka nan harda aikin farfado da tafkin Chadi da ruwa daga kasar Congo don taimakawa mutane fiye da dubu 30 wanda ya kafe shekaru masu yawa.
Shugaba Buhari ya bayana cewa sun gayyato shine don yazo ya zuba jari a matatar mai, wuta, noma, jirage, ilimi da abubuwa da dama. Ya kara da cewa yana so a farfado da Tafkin Chadin.
Kuma za’a samu a dawo da ayyuka kamar kamun kifi, noma, kiwo, samu aikin da matasa zasuyi ta dalilin ayyukan wanda hakan zai dauke hankulansu daga ta’addanci da hijira daga kasar.
Sheikh Hamad Al-thani yace yaji dadin yadda aka karbeshi a najeriya karon shin a farko, kamar yadda shugaba Buharin ya ziyarci kasar ta Qatar a shekarar 2016.
