Najeriya Ta Kafa Yaki Da Safarar Bil Adama

President-Miuhammadu-Buhari-wide-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta fidar da wani shiri na musamman domin dakile harkar safarar bin adama a sassan wannan ‘kasar.

Shugaban ya bayyana hakane a jaridar Washington Post na ‘kasar Amurka, wanda hakan ya yi dai dai da ranar tunawa da cinikin bayi da majalisar dinkin duniya ta 23 ga watan Agusta kowace shekara domin tuni da cikin bayi.

Hakazalika shugaba Buhari ya dana nanata cewa wannan tsarin da aka shigo dashi zai sanya jama’a yin tsanaki ga wadanda suke yi musu alkawarin wadatar rayuwa.

A karshe Buhari ya ce duk da dai babu wani tartibin hana wannan kangin bauta a zamanance, amma idan shuwagabannin ‘kasashen duniya suka jajirce za a dakile wannan matsalar.

Related stories

Leave a Reply