
Najeriya ta janye babban jakadan ta daga kasar Afirka ta kudu kuma ta janye daga taron kolin ci gaban kasashen duniya da za’ayi, a ranar laraba a Cape Town dake afirka ta kudun.
Cikin wata bayani da aka shaidawa manema labarai, gwamnati ta umarci ambasado Kabir Bala daya dawo gida, sannan gwamnatin ta nemi su biya diyar asarar rayuka da arzikin yan kasar sakamakon hare-hare na kin jinin bakin haure da yan kasar ke yiwa yan najeriyan.
Idan za’a iya tunawa, kasar Rwanda da DR Congo sun janye daga taron kwalin da za’ayin sakamokon hare-haren.

