Najeriya: Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Kalubalanci Shugabancin Jam’iyyar APC Da Gwamnonin APC Kan Kafa Jam’iyyar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kalubalanci shugabancin jam’iyyar APC da kuma gwamnonin APC kan bukatar a kafa jam’iyyar yadda zata rayu har bayan wa’adin sa ya kare bayan shekarar 2023.

shugaban ya bayyana hakan bayan da ya karbi gwamnonin na APC a fadar shugaban kasar dake Abujayayin da suka je taya shi murna kan nasarar da ya samu a shari’ar da aka gudanar kan zaben da aka gudanar.

haka nan ya kirayi shugaban jam’iyyar da gwamnonin kan su tabbata sun kafa jam’iyyar yadda ko basa nan zata cigaba da tasiri a kasar.

yayin da yake jawabi shugabn jam’iyyar Adams Oshiomhole ya bayyana cewa shari’ar an yita yadda ya kamata yadda zai kore duk wani zargi kan takardun makarantar shugaban kasar, Haka nan ya jaddada goyon bayansa da taimakonsa ga shugaban kasar.

shugaban gwamnonin jamiyyar Alhaji Atiku Bagudu, ya taya shugaban kasar murna kan nasarar da ya samu a shari’ar, san nan ya jaddada goyon bayan gwamnonin jam’iyyar gaba daya ga shugaba Buhari.

ya kara da cewa dukkkansu sun hallara ne don suyi murnar nasarar da aka samu kan shari’ar shugaban kasar wadda aka yanke ranar Laraba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *