Najeriya: Shugaban Karamar Hukumar Gubio Ya Ziyarci Sakatariyar Yankin

By: Adamu Aliyu Ngulde

Shugaban karamar hukumar Gubio Zannah Modu Gubio ya bayyana cewa a shirye yake ya samar da abubuawan more rayuwa ga mutanensa.

Zannah Modu Gubio ya bayyana hakan ne yayin da yake duba ayyukan da ake gudanarwa na fadada sakatariyar karamar hukumar da kuma fadada ofishin gudanar da allurar rigafi.

Haka nan ya yaba da yadda hukumar ayyuka ta karamar hukumar take aikin inda yace lafiyar mutane ce gaba da komai a gurin gwamnatin sa.

San nan ya ziyarci kauyen Mushallari dake yankin Ngetra a Gubio don duba makarantar firamare ta Kashim Shettima da iska ta lalata kwanan nan.

Ya kuma bukaci ma’aikatar ayyukan da ta fara gyaran rufin kwanon cikin kwana 3 don yara su samu su cigaba da karatu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *