Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Najeriya: Shugaban INEC Yace Sun Fara Shirin Zaben 2023

inec2 large
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban hukumar zabe na kasar najeriya farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana cewa hukumar ta fara shirye-shiryen zaben shekarara 2023 hade da gyara ga zaben da ya wuce na shekarar 2019.

Yakubu ya bayyana hakan yayin taron da suka gudanar kan duba yadda aka gudanar da zaben daya gabata da kwamishinonin zaben a Ikeja dake jihar Legas inda yace hukumar zata gyara wasu abubuwan.

Ya kara da cewa a cikin wata daya da rabi daya gabata ya gudanar da tarurruka 11 a tsakanin Abuja da Lagos kan zaben 2019, san nan ya bayyana cewa hukumar ta koyi abubuwa da dama da kuma inda zata sag aba a yanzu.

Haka nan ya bayyana cewa ‘yan siyasa sun kara bata abun inda suka yi zabe wasu guraren a dole, inda har aka kama batura zabe a wasu yankunan don su fadi sakamakon zaben dole.

Kwamishinan tsare-tsaren hukumar DR Mustapha Lekky ya bayana cewa wan nan tsarin da zasuyi shi zai basu damar zabukan da za’ayi a jihohin Bayelsa da Kogi da kuma zabukan da za’a gudanar a shekarar 2023.

Related stories

Leave a Reply