
Shugaban gidan yari na kasa Ahmed Ja’afaru ya hana kwamitin da gwamnatin jihar Borno ta gina bincike kan karuwancin yara, zubda ciki da wasu munananan dabi’u da ake gudanarwa a gidan yarin dake birnin Maiduguri.
Kwamitin yasha aika takardar tuni kan neman izini ga shugaban don yin binciken sakamakon rahoton da Sahara Reporters ta fitar amma shiru kake ji.
Shugaban shari’a na jihar kuma kwamishinan shari’a na jihar Borno Kaka Shehu Lawan ne ya bayyana hakan yayin da yake mika rahoton shi ga gwamnan jihar Kashim Shettima a gidan gwamnati.
Ya bayyana cewa kwamitin bai samu hadin kan jami’an hukumar ba daga babban ofishinsu na Abuja har dana Maiduguri.
Ya kara da cewa masu kare hakkin dan adam na da sha’awar wan nan rahoto inda suma suke jiran wan nan rahoto, gwamnan jihar ya jaddada cewa baza su bar wan nan zargin ya wuce ba tare da sun bincika ba.
Haka nan ya bayyana rashin jin dadinsa na yadda jami’an suka hana ayi binciken inda yace zai mika lamarin ga Ministan cikin gida Abdulrahman Dambazau ranar litinin.
