Najeriya: Shugaban Gidan Radiyo Dandal Kura International Ya Kaiwa Shehun Dikwa Ziyara A Maiduguri

Mai girma shehun Dikwa Alhaji Muhammad Ibn Shehu Masta na II ya bayyana shirye-shiryen gidan radiyon Dandal Kura International a matsayin masu mahimmanci.

Shehun ya bayyana hakan yayin da shugaban gidan radiyon Dandal Kura International Faruq Dalhatu ya kai masa ziyara a gidansa dake Maiduguri a jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya.

Shehun na Dikwa ya yabawa tashar kan ayyukan da takeyi na gina zaman lafiya a yankin tafkin Chadi, wanda mutane suka karba da hannu biyu saboda yaren da ake amfani dashi a yankin.

Shugaban ya samu rakiyar ma’aikatar gidan radiyon kamar su shugaban shirye-shirye Ibrahim Dahiru Biso, shugaban sashin labarai Babagana Bukar Wakil Ngala, shugaban kula da ma’aikata Habu Ahmed sai Muhammed Nur da Ali Muhammed Zanna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *