Najeriya: Shugaba Buhari Zai Taimakawa Wadanda Mbaliya Ta Shafa A Jihar Jigawa

President-Miuhammadu-Buhari-wide-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da taimakawa wadanda ambaliya ya shafa a yankunan jihar Jigawa inda yace gwamnatin zata taimaka.

Shugaban ya bada tabbacin tab akin babban mai taimaka masa ta fannin yada labarai da hulda da jama’a malam Garba Shehu a Abuja.

Haka nan yayiwa iyalan wadanda da suka rasa iyalansu ta’aziyya da jaje ga wadanda suka rasa gonakinsu da hanyoyin neman abinci jajen rasa kyayyaykinsu.

Shugaba Buhari ya umarci hukumar bada agaji ta kasa data samar musu kayan agaji a yankin.
San nan ya yabawa aikin gaggawa da hukumar ta jihar tayi yayin ambaliyar inda yace gwamnatinsa a shirye take ta taimaka.

Shugaban kasar ya bayyana cewa zai cigaba da bin rahotannin hukumomin bada agjin don daukar matakan gaggawa.

Manema labarai sun bayyana cewa kimanin mutane 19 suka rasu dubban gidaje suka suka rasa gidajensu.

Related stories

Leave a Reply