Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Najeriya: Shugaba Buhari Ya Amince Da Kafa Rediyo Da Talabijin Masu Amfani Da Yanar Gizo

buhari-talkingwidth-1-768x331
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

shugaba muhammadu buhari ya amince da a kafa rediyo da talabijin wanda zasu dinga amfani da yanar gizo a wani yunkuri na kawo gagarumin sauyi a harkan yada labarai.

wannan yana kunshe ne a wata sanarwa da mai bawa ministan yada labarai da al’adu shawara na musamman Segun Adeyemi ya fitar a Abuja.

sanarwar ta kara da cewa ministan yada labarai Lai Mohammed shi ya fadi hakan a yayin da yake karban bakwancin yan kungiyar kafofin yada labarai ta Najeriya.

Muhammed ya kara da cewa shugaban kasa ya kuma yarda da yan kasashen waje suma su rika hasko shirye-shiryen su domin a dada kara bunkasa al’amarin yada labarai, inda ya kara da cewa za’a say an kungiyar a cikin kwamitin da zai sake duba dokokin da suka shafi yada labarai a kasan nan.

A nashi tsokacin, mai rike mukamin shugaban kungiyar Sir Godfrey Ohuabunwa, yace sake nada Lai Muhammad a matsayin ministan yada labarai ya nuna irin cancantar sa a wannan mukami kuma yana fatan zai kawo sauye-sauye a harkar yada labarai.

Related stories

Leave a Reply