Najeriya: Shugaba Buhari Bai Kaskanta Mataimakinsa Ba

buhari-osinbajo
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Mataimakin shugaban kasa na mussamman kan lamuran majalisar Sanata Babajide Omoworare, ya bayyana cewa shugaba Muhammadu Buhari bai aika da wasika cewa mataimakinsa Farfsa Yemi Osibanjo zai cigaba da jan ragamar mulki a madadinsa ba.

Sanata Omowarare ya bayyana haka yayinda yake jawabi ga manema labarai a birnin tarayya Abuja inda ya ce shugaba Buhari na da ikon gudanarda mulki a ko ina.

Cikin jawabinsa shugaban jam’iyyar APC Kwamared Adams Oshiomhole shima ya ce shugaba Muhammad Buhari zai iya cigaba da jar ragamar mulki a duk inda yak e.

A nasa 6angaren babban mashawarcin shugaban ‘kasa kan al’amuran da suka shafi ‘yan majalisar tarayya Mista Umar El-Yakub, ya bayyana shugaba Buhari a matsyain mai ‘kokarin wanzarda kyakkyawar shugabanci.

Mashawarcin shugaban ya jaddada cewa abinda zai sa mutane su yi magana shi ne saidai idan shugaban ba shida lafiya idan bayanan.

Related stories

Leave a Reply