
By: Babagana Bukar Wakil Ngala
Mai girma Shehun Borno Dr. Abubakar Ibn Garbai Al-Amin Elkanemi ya kirayi mutane dasu kai rahoton duk wani da basu yadda dashi ba ga jami’an tsaro don a samu a kawo karshen ta’addanci a jihar da kasa baki daya.
Shehun ya bayyana hakan bayan an idar da sallar idi a filin Ramat Squares dake birnin Maiduguri inda daga bisani ya gudanar da hawan sallar da hakimansa.
Gwamnan jihar farfesa Babagana Umara Zulum, Sanata Muhammed Ali Ndume da masu ruwa da tsaki na daga cikin wadanda suka halarci bikin.
Dubban mutane ne suka halarci bikin inda wasu ma sun dade basu halarta ba sakamakon rikicin Boko Haram.
Haka nan Shehun ya kirayi jama’a dasu guji sare bishiyoyi ba bias ka’ida ba inda ya bukaci gwamna Zulum daya karfafa abun don a ceci mutane.
