Najeriya: Shehun Borno Ya Yabawa Gidan Radiyon Dandal Kura

Shehun Borno, Dr Abubakar Ibn Umar Garbai ya yabawa gidan Radiyon Dandal Kura International kan kokarin da take na yaki da ta’addanci.

Shehun ya bayyana hakan bayan da ya karbi bakuncin shugaban gidan radiyon a fadar sa dake birnin Maiduguri, a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya.

Ya yaba musu kan kokarin da suke na gina zaman lafiya da samar da maslaha.
Haka nan ya bawa tashar shawara kan ta dage dantse wajen ilmantar da mutane kan su dinga kula kuma su kai rahoton duk wanda basu yadda dashi ba ga jami’an tsaro.

Dr. Abubakar Ibn Umar Garbai ya kirayi shugaban kasar najeriya Muhammadu Buhari kan nauyin dake kansa na yaki da yan kungiyar Boko Haram a yankin.

San nan ya bayyana cewa yana da yakinin cewa za’a kawo karshen ta’addancin nan ba da dadewa ba kamar yadda na Maitatsine da Rabe suka wuce.

Shugaban gidan Radiyon na Dandal Kura International, Faruq Dalhatu, ya bayyana wa Shehun cewa ya kawo masa ziyara ne don ya bayyana masa cewa sun bude tashar FM ne kan mita 98.9.

Shugaban ya samu rakiyar shugabannin shirye-shirye, sashin labarai da shirye-shirye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *