Najeriya: SEMA Ta Karyata Rahoton Cewa Kan Rashin Abinci Aka Yi Zanga-Zanga

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno wato SEMA ta karyata rahoton da ake yadawa kan cewa yan gudun hijirar dake sansani na Gubio a Maiduguri sun gudanar zanga-zanga ne saboda rashin abinci.

Shugabar hukumar ta SEMA Hajiya Yabawa Kolo ta bayyanawa manema labarai cewa zanga-zangar ba don rashin abinci ko yunwa bane sun gudanar da zanga zangar saboda rashin basu kayan abinci da aka saba na wata akan lokaci ne wanda yan kungiyar sa kai suke bayarwa.

Kolo ta kara da cewa hukumar na aiki da kungiyar abinci ta duniya wato WFP, NEMA, ICRC, AAH don samar da abinci ko wane wata a sansanonin dake Maiduguri.

Ta kara da cewa SEMA na samar da danyen kaya inda ragowar suke samar da kayan abinci. Ta kuma bayyana cewa yan gudun hijirar dake sansanin sun fito ne daga arewacin jihar kamar kananan hukumocmin Kalabalge da Kukawa.

kolo kuma bayyana cewa suna iyakar kokarinsu kuma duk inda za’ace zaka kula da mutane kimanin miliyan daya 1.4 dole a samu jinkiri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *