Najeriya: Sarkin Musulmi Ya Kirayi Jama’a Dasu Fara Duban Sabon Watan Ramadan

Sarkin musulmin Najeriya kuma Sultan na Sokoto dake Rewa maso yammacin kasar Muhammad Sa’ad Abubakar III ya kirayi musulman kasar da su fara duban watan Ramadan na shekarar 1440 bayan hijira ranar Lahadi.

Ya bayyana cewa 5 ga watan May una shekarar 2019, wanda yazo dai-dai da 29 ga watan Sha’aban, 1440 bayan hijira ya zama ranar da za’a duba sabon watanRamadan na shekarar 1440 bayan hijira.

Hakan na kunshe a rahoton da shugaban kwamitin harkokin musulinci farfesa Sambo Junaidu inda yace jama’a su bayyanawa shugabannin kauyukan su yayin da suka ga sabon watan.

Haka nan ya shawarci Kwamitin ganin watan da su fara duban watan na Ramadan bayan faduwar ranar ranar Lahadi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *