Najeriya: Sarki Sunusi Ya Bukaci Yan Jarida Dasu Dinga Aiki Bisa Doka Da Kwarewa

emir-kano-sanusi-lamido
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II  ya bukaci yan jarida dasu dinga aiki bisa doka da kwarewa, inda ya yi kira garesu dasu bi ka’idojin aikinsu don cigaban kasar.

Sarkin yayi kiran a fadarsa yayin daya karbi bakuncin mahukuntan gidan jaridar ‘The Reporters Magazine’ wanda suka je don bashi lambar yabo.

Sanusi yace ba abinda ake bukatar dan jarida dashi wajen gudanar da aikinsa irin rike gaskiya akowane lokaci.

Ya kara da cewa ya kamata gidan jaridu su Dage wajen fadar gaskiya da kuma bin dokokin aikin nasu a koda yaushe.

A nashi jawabin shugaban masu tace labarai na gidan jaridar ta The Reporters Magazine, MallamAbdullahi Sabiu ya bayyana wa sarkin cewa mahukuntansu sun yanke shawarar karrama sarki saboda gudunmawar da yake bayarwa wajen gina kasar.

Related stories

Leave a Reply