Najeriya: Osinbajo Ya Kaddamar Da Aikin Wuta Mai Karfin Megawatts 7.1 A Jami’ar Bayero

Yemi-Osinbajo small 2
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kaddamar da aikin wuta mai karfin megawatts 7.1 a jami’ar bayero dake kano domin samar da isasshen wutan lantarki cikin jam’iar.

Osinbajo yace aikin zai amfani dubban dalibai da kuma inganta fannonin koyarwa, bincike, da karatu. Yakara da cewa, akalla jami’o’i 37 a fadin kasar zasu samu wannan ci gaba sannan hakan zaiyi sanadiyar samar da ayyukan yi da kuma ci gaban karatun ya’ya mata wanda manyan muradin ne cikin ayyukan gwamnatin shugaba Buharin.

Datake jawabinta, daractan kungiyar samar da wutan lantarki Damilola Ogunbiyi tace an samar da wannan ci gaban ne domin kawo karshen yankewar wuta.
.
Haka zalika mataimakin shugaban jami’ar farfesa Muhammad Yahuza-Bello ya yabawa gwamnatin da samar da wuta mafi karfi datayi a jami’ar.

Related stories

Leave a Reply