Najeriya: Na Tura Sakamakon Zabe Kundin Hukumar Zabe – Baturen Zabe

Baturen zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 23 ga watan Fabarairu Adejuyitan Olalekan, ya bayyana ranar Litinin cewa ya aika sakamakon zaben da aka irga a mazabarbarsa zuwa kundin hukumar zaben ta kasa.

Olalekan ya bayyana wa kotun sauraron karar zaben shugaban kasar dake Abuja yayin da yake bada shaida wanda shine shaida na 3 na dan takarar na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.

Yayin shari’ar da Dr. Livy Uzoukwu (SAN) ya jagoranta, Shaidan daya gabata kafin shi zai yi rantsuwa saboda bai bayyana gari ko mazabar da ya gudanar da aikin ba yayin zaben.

Yayin shari’ar Lauyan Muhammadu Buhari shine Chief Wole Olanipekun (SAN), wani mai shaida ya bayyana cewa shi malami ne a African Community of Inquiry College of Education dake jihar Enugu State ya bayyana cewa shima ya tura sakamaon zaben mazabarsa ta hanyar da hukumar zaben ta INEC ta bayar.

Yayin da Lauyan hukumar INEC Yunus Usman (SAN) ya tambayeshi Olalekan ya bayyana cewa bai da suna ko lambar kundin.

An kara tambayarsa ko yana da bayanan yadda ya tura bayanan ya bayyana cewa bai da su a yanzu amma suna wayarsa.

Yayin da Olanipekun yake tambayarsa mai shaidar ya tabbatar da cewa duk wadanda suka yi zabe a mazabarsa sunyi ta hanyar Katin zabe kuma injinan na aiki yadda ya kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *