Najeriya Na Da Yawan Mutanen Dake Shan Magani ba Bisa Ka’ida Ba – NAFDAC

NAFDAC
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By:Yabawa Ismaila Borno
Hukumar yaki da amfani da magunguna ba bisa ka’ida ba wato NAFDAC ta jawo hankali kan yawaitar amfani da magungunan ba bisa ka’ida ba a Najeriya.

Hukumar ta lura cewa Najeriya na kan gaba da da kashi na biyar na kasar da take amfani da magungunan ba bisa ka’ida ba kuma tana da kasha goma sha biyar na masu shaye-shayen.

Daraktan hulda da jama’a na hukumar ta NAFDAC, Dr. Abubakar Ateiza Jimoh, ne ya bayyana hakan yayin da yake ganawa da manema labarai a garin Ilorin dake jihar Kwara.

Jimoh yace akwai a kalla mutane miliyan 15 da suke shan kwayoyin inda kimanin miliyan 3 sun maida shi al’adar su.

Haka nan hukumar ta dora laifin shan magungunan da ummul aba’isin yawaitar rikice-rikice, garkuwa da mutane, ta’addanci, fashi da makami, tukin ganganci a najeriya.

Daraktan NAFDAC na kwamitin shugaban kasa kan yaki da shan magungunan Buba Marwa, yace kwamitin na nan na ganin yadda za’a kawo karshen lamarin.

Related stories

Leave a Reply