Najeriya: Mutanen Mairi Kuwait Dake Jihar Borno Sun Koka Kan Sababbin Hare-Hare A yankin

borno-state-small
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Wani shugaban yankin Mairi-Kuwait dake karamar hukumar Jere a jihar Borno Malam Usman Yaya ya bayyana matsanancin halin da suke ciki na rashin tsaro da yawaitar hare-hare ga manoman yankin da suke neman abinci.

Yayin da yake Magana da gidan radiyon dandalkurain a Maiduguri, MalamYaya yace a yankin nasu suna binne kimanin mutane biyu ko uku a kowace rana.

Ya kara da cewa akwai fiye da yan gudun hijira 7,500, inda suna da kimanin magidanta 12,765.

Ya kuma bayyana cewa a shekaru 6 da suka gabata, tunda yan gudun hijira suka dawo gida talauci ya karu a yankin saboda ba wani tallafi da suke samu daga gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu.

San nan ya bayyana cewa binne mutane a kowace rana ya zamar musu jiki don haka ya kirayi gwamnati data karo musu sojoji musamman a gurare masu hatsari da guraren da suke da hanyoyin da suke hade da dajin Sambisa don dakile ayyukan yan ta’addan.

Related stories

One comment

  1. I’m also an indigenous of Mairi Kuwait,our main issues is that, whenever we’re going to farm we are scary on our way either one or two things may happen,either Boko Haram, Human traffickers or Armrobbers .. please we need more security especially behind University of Maiduguri because most times this people used to appears….

Leave a Reply