Najeriya: Mutanen Jikum A Jihar Taraba Sunyi Kira Da A Kara Musu Jami’an Tsaro

Mutanen jikum dake jihar Taraba a Arewa maso gabashin Najeriya sun kirayi gwamnatin tarayya da ta jiha dasu kara tura musu jami’an tsaro kauyukan da akwai yiwuwar kai hari don a samu zaman lafiya da akre rayuka da dukiyoyin jama’a.

Iliya Ibrahim Agabi daya daga cikin yan kabilar dake a Wukari ne yayi kiran yayin da yake Magana da wakilin gidan Radiyon Dandal Kura a Jalingo Ahmed Umar Gasol.

Ya bayyana cewa jukun sunki yadda yadda da kabilar Tivi a cikin al’adunsu. Haka nan ya bayyana cewa yakamata gwamnati ta dauki matakai don shiya wan nan rikicin.

Ya kuma kirayi jami’an tsaro dasu gurfanar da masu laifi gaban hukuma, kuma gwamnati ta bawa wadanda abun ya shafa kayan agaji da kuma gyaran garin Chonku da Kente da Tiv suka lalata.

Shugabancin al’adun Tiv Cultural da walwala wanda shugabansu Chief Goodman D. Dahida yake wakilta ya bayyana yadda ake ware yan kabilar Tiv daga masarautar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *