Najeriya: Ministan Noma Ya Yaba Da Rufe Iyakokin Kasar

Nanono
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Ministan noma Alhaji Sabo Nanono ya bayyana cewa kudurorin da gwamnatin tarayya ta gabatar musamman na rufe iyakokin kasar na daya daga cikin kudurorin masu amfani wanda hakan zai kawo samun wadacccen abinci.

Nanono ya bayyana hakan a Kaduna yayin bude taron shekara-shekara na 49 wanda injiniyoyin hada sinadarai mai taken habbaka ayyukan ayyukan noma don cigaban tattalin arziki da kuma yadda injiniyoyin ke taka rawarsu.

Ministan ya kara da cewa an gabatar da kudurorin don dakile  shigo da kayyayyaki daga kasashen waje don a karfafa wadanda kasa take sarrafawa da kuma samar da ayyuka gay an kasa.

San nan ya bayyana cewa an dangana cigaban Najeriya akan hanayar noma, wanda shi kadai ne zai kai kasar mataki na gaba kuma yaci gaba habbaka tattalin arzikin kasar.  

Haka nan rahoton ya nuna yadda a shekarar 2017 noman shinkafa yake a tan miliyan 3.7 inda ana sa ran nan da shekara 5 zai kai tan miliyan 7.2.  

Yayin da yake jawabi a gurin taron shugaban kungiyar Injiniya Onoche Anyaoku ya bayyana cewa an zabi taken taron cikin tsanaki don lura da ake fama da matsalar tattalin arziki a kasar inda akwai bukatar wadatar dukiya tsakanin al’umma, samar da ayyuka, da kuma masu zuba jari don samun wadatuwa ga al’umma, wanda shine kudirin gwamnatin.

San nan ya kara da cewa yadda ake gudanar da ayyukan noma a kasar nan bai canza ba tun kafin a samu yancin kai.

Related stories

Leave a Reply