Dandal Kura Radio International Kanuri: Kowu’o Fal Kanuri Milion Mew’wu Kla
Kanuri Miliyan Goma, Murya Daya
Dandal Radio 98.9FM Voice for Peace
Dandal Kura FM 98.9 Kowo’u nabtu N3l3fay3
Dandal Kura FM 98.9 Muryan Zaman Lafiya

--:--
--:--
  • FM Stream
  • Shortwave

Najeriya: Ministan Babban Birnin Tarayya Ya Bayyana Cewa Akwai Tsaro Sosai A Abuja

Abuja
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Duk da yawan samun rahoto da akeyi na cewa ana yawan yin garkuwa da mutane a babban birnin tarayya Abuja, Ministan babban birnin Mallam Muhammad Musa Bello ya bayyana cewa birnin yana cikin tsaro amma ya kamata jama’a kar su bar hukumomin tsaro su kadai wajen magance wadan nan matsalolin.

Ya bayyana hakan a rahoton daya fitar ta bakin sakataren yada labaransa CPS, Anthony Ogunleye.
Ministan ya bayyana hakan bayan taron da suka gudanar na tsaro akan Abujan wanda ya hada da shugabannin yansanda, sojoji, da ragowar hukumomin tsaro dake birnin ciki har da shugabannin yakuna da malaman addinai.

Bello, ya kara da cewa yana da matukar wahala ace jami’an tsaro zasu zama suna ko ina dari bisa dari, don haka ya kamata mazauna birnin su sa ido.

Kuma ya kirayi al’umma dasu dena yada jita jita musamman a kafafen sada zumunta su dinga tabbatar da abu kafin su wallafa.

Haka nan akan sha’anin rikicin yankuna Bello ya yabawa shugabannin yankuna da sarakunan gargajiya wajen kawo karshen rikicin manoma da makiyaya.

A nashi bangaren Kwamishinan yansandan birnin ya bayyana cewa masu aikata wadan nan laifukan na amfani da layikan da basu da rigista da kuma tasi mara sa fenti don haka sun hada kai da hukumar sufuri don kama masu laifin.

Related stories

Leave a Reply