
Sakatare Janaral na majalisar dinkin duniya ya bayyana cewa kungiyoyin sa kai din nan guda biyu Action against Hunger da Mercy Corps, wadanda jami’an sojin Najeriya suka dakatar a watan satumba sakamakon zargin hada baki da Boko a a Arewa maso gabashin Najeriya zasu koma bakin aiki a kwanakin nan.
Ya bayyana hakan ne bayan day a karbi tabbaci daga mahukuntan da abun ya shafa.
Hulda tsakanin najeriya da kungiyoyin masu zaman kansu yayi kamari ne watan day a gabata bayan da jami’an soja suka rufe ofisoshinsu dake Borno da Yobe inda suke zarginsu da taimakawa mayakan Boko Haram.
Yayin da Mr. Lowcock ya ziyarci jihar Borno ya bayyana yanayin mutane yake a jihohin Borno, Adamawa and Yobe, inda ya yabawa gwamnatin najeriya da jami’an tsaro wanda suka sa baki kan rashin fahimtar da aka samu.
Ya kara da cewa yana fatan ganin kungiyoyin sun dawo bakin ayyukansu don cigaba da gudanar da ayyukan taimako ga mtanen da rikicin ya shafa.
San nan ya bayyana cewa yaba da yunkurin gwamnati kan yadda tace zata gana da masu ruwa da tsaki, majalisar dinkin duniya da kungiyoyi masu zaman kansu na gida dana kasashen waje don samun zaman llafiya da kare fafaren hula a Arewa maso gabas.
