
BY: Aisha SD Jamal, Maiduguri
Watan Ramadan wata ne da musulmai suke azumi a ciki daga Safiya zuwa faduwar ranar don kusantar Ubangijinsu.
A jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya, wan nan karon ya shigo cikin matsannancin zafi inda mutane ke azumin cikin yanayi na zafi.
Dandal Kura sun lura cewa jihohin Adamawa, Yobe, Sokoto, Abuja da wasu jihohinma na fuskantar wan nan yanayin.
Haka ma a wasu kasashen kamar Ghana, Chadi, Kamaru, Nijar da sauransu, inda suke fuskantar yanayin safe da kuma dare.
Wani mai suna Muhammad Alkali dan shekara 25 ya bayyana cewa bai taba fuskantar irin wan nan yanayin ba a watan na Ramadan.
