Najeriya: Mazauna Birnin Maiduguri Zasu Fara Amfani Da Kwandunan Zuba Shara A Ko Ina

borno
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

By Adamu Aliyu Ngulde

Mazauna birnin Maiduguri babban birnin jihar Borno a Arewa maso gabshin Najeriya zasu fara amfani da kwandon zuba shara a guraren gwamnati dama bana gwamnati ba don gyaran muhalli.

Komandan muhalli na kasa Mr. Charles Joshua ne ya bada shawarar yayin da ya kawo ziyara jihar
Ya bayyana cewa idan aka lura da muhimmancin muhalli ta bangaren lafiya ya kamata a fara amfani da kwandon sharar don gyaran muhallin.

Haka nan ya bawa hukumar ta BOSEPA shawarar da su yi kokarin ganin sun kare duk wani abinci ko ruwa daga hanyoyi mara sa kyau kuma su mika masu laifi gaban kuliya.

A wata hira da gidan Radiyon Dandal Kura International Malam Mustapha na unguwar Gwange, ya bukaci gwamnati data samar da kwandunan zuba sharar don a tsaftace muhallan.

Related stories

Leave a Reply