Najeriya: Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba Ya Kirayi Musulmai Da Wadanda Ba Musulmai Ba Dasu Hada Kansu

taraba deputy governor
Share on facebook
Share on google
Share on twitter
Share on linkedin

Mataimakin gwamnan jihar Taraba Alh. Haruna Manu ya kirayi musulman jihar dasu dage da addu’oin kawo karshen rikicin kabilanci da ragowar matsalolin tsaro dake addabar jihar.

Mai rahoton radiyo Dandal Kura dake jihar ya bayyana cewa bayan an idar sallar Idin da aka gudanar a filin idi na jami’ar jihar mataimakin gwamnan Alh. Haruna ya kirayi mutane da su rungumi zaman lafiya.

Ya kara da cewa lokacin sallar lokaci ne da musulmai da wanda ba musulmi ba ya kamata su hada kansu su dena yin duk wani abu da zai haddasa rikici.

Related stories

Leave a Reply