Najeriya: Mataimakin Gwamnan Jihar Borno Ya Yabawa Dangote

Mataimakin gwamnan jihar Borno dake Arewa maso gabashin Njaeriya Usman Durkwa, ya yabawa shugaban gidauniyar kamfanin Dangote Alhaji Aliko Dangote da manajan daraktar kamfanin Mrs. Zoiera Youssoufou, saboda taimakon kayan abinci da suka bayar na kimanin Naira miliyan 200 don a rabawa mutane musamman yan gudun hijira a wan nan watan na Ramadan.

Mataimakin gwamnan ya yaba musu yayin da ake kaddamar da kayayyakin a kananan hukumomin Konduga da Bama.

Durkwa wanda ya wakilci gwamnan jihar Kashim Shettima ya bayyana cewa gwamnati da al’ummar jihar Borno na matukar godiya da wannan taimakon na gidauniyar Dangote a wannan watan na Ramadan

Gidauniyar ta Dangote tana taimakawa da kayan abinci ko wace shekara wanda hakan na rage samun karancin abinci a jihar Borno kuma mutane na matukar godiya da nuna jin dadinsu.

Haka nan mataimakin gwamnan ya kirayi jama’a da suyi amfani da wan nan watan suyi addu’ar zaman lafiya a jihar Borno da kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *