
Masu ruwa da tsaki a yankin Arewa maso Gabas a yayin taro game da matsalolin tsaro sun bukaci gwamnatin tarayya da ta ‘kara kudaden da dakarun soji, jami’an ‘yan sanda da ma sauran jami’an tsaro suke samu domin yaki da ta’addanci da kuma sauran nau’ikan ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.
Daga ‘karshe yayin taron kwana da aka gudanar a dakin taron na Multipurpose dake gidan gwamnati anan birnin Maiduguri an cimma matsaya game da wasu batutuwa sha hudu.
Da yake jawabi gwamnan jiha Farfesa Babagana Umara Zulum ya bukaci dakarun soji, jami’in ‘yan sanda da ma sauran jami’an tsaro da su bada hadin kai domin a cigaba da ya‘kar ta’addanci.
Mahalarta taron sun bayyana cewa akwai bukatar hukumar raya yankin Arewa maso Gabas ta tallafawa gwamnonin Arewa maso Gabas, da kuma samarda kayayyan aiki ga jami’an ‘yan sanda da kuma sauran jami’an tsaro.
Taron ya kuma ‘karawa mahukunta a matakai daban-daban ‘kwarin gwiwa da zauna teburin sulhu da ‘yan ta’adda saboda hakan zai kasance mafi a’ala ga sauran wadanda suke da niyyar mika wuya.
