
Makarantar rundunar tsaron najeriya ta NDA ta gargadi jama’a dasu kiyayi yan damfara da suke cewa sune jami’an bada gurbi a makarantar.
Jami’in hulda da jama’a na makaranatr ta NDA Major Abubakar Abdullahi ne ya bayyana hakan a rahoton daya fitar inda ya bukaci da masu neman shiga makarantar su kula.
Yace yan damfarar sun buga takardar shaidar bada izinin karatu na bogi suna rabawa mutane suna karbar kudi.

