
Mabarata sun cika lunguna da sakon cikin birnin Maiduguri sakamakon rikicin Boko Haram.
Wakiliyar gidan Radiyon Dandal Kura Aisha SD Jamal ta zanta da wasu daga cikin mabaratan wanda suka bayyana mata cewa bara itace hanya kadai da zasu samu abinda zasu kula da kansu duk da yawan kungiyoyi masu zaman kansu da ake dasu a jihar.
Wani magidanci mai suna Babagana Ngwali ya bayyana mata cewa yana bara ne don ya samu abinda zai kula da iyalinsa, haka nan wata mai suna Fatima Binta ta bayyana cewa bata da lafiya ne kuma bata da mai taimaka mata shiyasa take bara.
Wan nan rahoton ya nuna cewa masu barar sun hada da matasa, yara, tsofaffi maza da mata, da suka bar kauyukansu saboda rikicin ta’addanci.
Haka nan wata budurwa da muka samu tana bara da kannenta maza 3 ta bayyanawa gidan Radiyon Dandal Kura cewa tana bara ne don basu da kowa kuma don su kula da mahaifiyarsa da bata da lafiya.
Mabaratan dai sun bukaci gwamnati da yan kungiyoyi masu zaman kansu dasu taimaka musu a matsayinsu nay an Najeriya.
