Najeriya: Kwamitin Sabbabin Makarantun Jihar Borno Ya Fara Tantance Dalibai

By Adamu Aliyu Ngulde.

Kwamitin kaddamar da marakarantun zamani da gwamnatin jihar Borno dake Arewa maso gabashin Najeriya ta gina ya fara tantance marayu da wadanda iyayensu basu da karfi a sansanonin yan gudun hijira don su shiga makarantun.

Karamin kwamitin ya fara tantance yaran ta hanyar daukar bayanan su a injina masu kwakwalwa a sansanin yan gudun hijira na Bakassi dake birnin Maiduguri.

Gwamnatin jihar dai ce ta gina makarantun don a farfado da ilimi da kuma taimakawa mara sa karfi da wadanda suka rasa mahallansu da sakamakon rikicin Boko Haram.

Sheikh Tijjani Umara ne ya jagoranci kwamitin tantance yaran da suka dace a sansanin. Haka nan shugaban kwamitin ya bayyana cewa ana samun nasara akan aikin.

Sa’an nan kwamitin zai duba wasu yankunan da akwai marayu da marasa galihu ya zabo suma a sakasu a makarantun bayan an dauki bayanan su a injina.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *